An sami raguwar mutuwan yara da ke dauke da cutar Bakon Dauro a Najeriya amma har yanzu yaran da ba a musu alluran rigakafin cutar ba ya go yawa a Najeriya.
Kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya ta ruwaito cewa a duniya gaba daya yara miliyan 20.8 ne ke fama da matsalar rashin yin allurar rigakafin cutar Bakon Dauro sannan mafi yawan yaran na zama a kasashe 6 da ya hada da; Najeriya da ke da yawan yara miliyan 3.3 sai Kasar India da ke da yara miliyan 2.9, Pakistan na da miliyan 2.0, Indonesia na da miliyan 1.3, Ethiopia na da 900,000 sannan Jamhuriyyan Kongo na da 700,000.
Bisa ga bincike da asusun UNICEF ta yi ya nuna cewa cutar bakon dauro da aka fi yi lokacin zafi ya karu a yankin arewacin Najeriya tsakanin shekaru 2014 zuwa 2016.