Shugaban majalisar dattijai , Bukola Saraki ya ce bai karya dokar Najeriya ba mallakar kamfanin Tenia Limited a tsibirin Cayman, dake yankin Caribbean.
A wata takarda da mai taimaka masa kan harkar yada labarai Yusuf Olaniyonu ya sanya wa hannu, Saraki ya ce ba da gangar bane bai lissafo wannan kamfani da yake bada bayanan shaidar kadarorin sa ga hukumar kula da da’ar ma’aikata.
” Wannan kamfani an kafa ta ne a 2001 tun kafin Saraki ya fara harkar siyasa.
” Kamfani da tunda aka kafa ta ba a taba amfana da ita ba. Bata da asusun ajiya na banki, bata da wani kadara ballantana ace wai anyi amfani da ita wajen harkallar kudade.
” Sannan kuma ku sani cewa duk abin da ake bukata Saraki ya yi na zayyano abubuwan da ya mallaka duk ya yi, babu dokar da ya karya.
Olaniyonu ya ce bisa ga dukkan alamu, Saraki ya manta da wannan kamfani ne tunda babu abinda da akeyi da ita.
A cikin 2001, Saraki ya kafa wani kamfani mai suna Tenia Limited can a Tsibirin Cayman, a yankin Caribbean. Ya ci gaba da rike shugabancin kamfanin a matsayin darakta, wanda kuma shi kadai ne ke da hannun jari a cikin sa.
Sai dai kuma inda matsalar ta ke, shi ne Saraki bai lissafa Tinea Limited a cikin jerin kadarorin da ya mallaka ba, a lokacin da aka zabe shi a matsayin gwamnan jihar Kwara cikin 2003.
Hakan ya na nufin cewa kuru-kuru Saraki ya karya dokar CCT. Haka nan Saraki bai lissafa da sunan kamfanin ba a 2007 lokacin da aka sake zaben sa gwamna da kuma 2011, da kuma lokacin da aka zabe shi Sanata.
Wannan sabuwar fallasa da aka yi wa Saraki da sauran dimbin wasu shugabanni na duniya, ya fito ne daga tonon-sililin-zare da wata jaridar kasar Jamus mai suna Suddeutsche Zeitung tare da hadin guiwa da ICIJ suka yi, daga cikin wani bayanin sirri da ya fito daga wata kafar soshiyal midiya mai tara bayanan sirri, wato Appleby and Trust.
Gidan jaridar PREMIUM TIMES ne kawai yake da izinin samun wadannan bayanai a Najeriya.
Discussion about this post