Ba za mu dawo da Abdulmumini ba sai ya roki majalisa – Majalisar Wakilai

0

Majalisar Wakilai ta sanar da cewa ba za ta amince dan majalisa Abdulmumini Jibrin ya dawo majalisar ba sai ya rubuto lafiyayyar wasika a ciki ya roki a yafe masa tukuna kafin a yarda masa ya dawo don ci gaba da Zama a zauren majalisar.

Majalisar ta dakatar da Abdulmumini Jibrin na tsawon kwanaki 180 saboda yi wa shugaban majalisar da wasu ‘yan majalisa kazafin yin sakale a kasafin kudin 2016.

Duk da cewa kwanakin dakatarwar ya cika kakakin majalisar AbdulAziz Namdas ya ce har yanzu Majalisar na nan akan bakan ta na sai ya roke ta kafin ya dawo zauren majalisar.

Share.

game da Author