Atiku ya fice daga APC

0

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya fice daga APC.

Atiku ya sanar da haka ne a wata sanarwa da ya aika wa PREMIUM TIMES a safiyar Juma’a.

Atiku ya ce dama can ya shiga jam’iyyar APC domin a gyara kasa amma abin da kamar wuya.

” Ba zan iya zama a jam’iyyar da ba su damu da matasa ba da ci gaban kasa. Saboda haka bayan na gama duk shawarwari na na ga ba zan iya ci gaba da zama dan jam’iyyar APC ba.”

Ya ce zai yi shawarar inda ya dosa nan ba da dadewa ba

Share.

game da Author