APC da PDP duk Kame-Kame su keyi – Inji Obasanjo

0

Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya ce har yanzu bai ga wani abin azo agani ba a gwamnati mai ci sannan ita ma jam’iyyar PDP din duk kwashikwaraf ne.

Obasanjo ya fadi haka ne da ya ke amsar bakuntar shugaban gidan talabijin na AIT kuma dan takaran shugaban jam’iyyar PDP a dakin karatun sa a Abeokuta.

” Abu daya da na sani shine duk jam’iyyun na da dama su gyara kan su domin zama jam’iyyun da za a iya alfahari da su.

” Idan kuna ganin cewa hukuncin da kotun koli ta yanke shine samun lafiya a jam’iyyar PDP, to ku sani hakan bai yi ko kusa da samun lafiyar ku ba. Ita kotun koli tayi aikin ta ne kawai, gyaran jam’iyya sai kun zauna da kanku kun gyara.

Ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar da su tabbata sun zabi shugaban nagari a zaben jam’iyyar da ke zuwa, cewa haka ne kawai zai sa su kai ga ci.

” A zamani na sai da nayi shugabannin jam’iyya har 4, saboda haka na san dadi da rashin dadin samun shugaba nagari da wanda ba nagari ba.

Share.

game da Author