An daga gurfanar da tsohuwar Babbar Daraktar Aso Saving and Loans, Maimuna Salihu, daga yau Talata zuwa 5 Ga Disamba, 2017.
Muhutin Alkali ne ya shaida wa Lauyoyi da ‘yan jaridu haka a yau Talata, cewa mai shari’a ya na halartar wani kwas, wanda hakan ne ya tilasta dage zaman sauraren shari’ar yau.
PREMIUM TIMES a yau ta tabbatar cewa Maimuna ba ta halarci kotun a yau ba.
Ana zargin ta karkatar da kudi naira miliyan 57 daga asusun Aso Savings and Loans.
Hukumar ICPC wadda ita ce za ta gurfanar da ita a kotu, ta ce kudin na daga cinikin da aka yi na sayar da wasu filaye uku a Abuja.
Maimuna dai ita ce mahaifiyar Maryam, matar da ake zargin ta kasha mijin ta cikin makonni biyu da suka gabata.