Tsohon shugaban gidan rediyo na tarayya, Ladan Salihu wanda haifaffen jihar Bauchi ne ya bude sabuwar gidan rediyo mai zaman kanta na farko mai suna Albarka fm a garin Bauchi.
An fara gwajin watsa shiye-shirye a wannan sabuwar gidan radiyo Albarka fm 97.5 fm ranar 1 ga watan Nuwamba a garin Bauchi.
Da yake gwajin hakan Ladan Salihu ya amsa kira daga mutanen jihar domin sanin yadda suke kama tashan a wannan lokaci da aka fara gwajin watsa shirye-shirye daga tashar.
Za a iya kama tashar ne a a garin Bauchi.
Discussion about this post