Tsohon mataimakin shugaban kasa Alex Ekweme ya rigamu gidan gaskiya.
Kamar yadda iyalan mamacin suka sanar a jaridar Sun, Alex ya rasu ne a wani asibiti dake Kasar Britaniya.
Idan ba manta ba a makon da ya gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin kai sa kasar Britaniya domin likitoci su duba shi.
Alex ya rasu ne a daren jiya Lahadi. Shine mataimakin tsohon shugaban kasa Alh. Shehu Shagari a jamhuriya ta biyu.