Abin da El-Rufai ya keyi kan maganar Ilimi a Kaduna abu ne mai kyau – Buhari

1

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yaba wa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai kan gyaran da ya ke yi a fannin Ilimin jihar.

Buhari ya fadi haka ne a taron farfado da harkar ilimi a kasar nan da ya halarta a safiyar litinin a dakin taro dake fadar gwamnati.

Buhari yace tabarbarewar Ilimi a kasar nan abu ne da yake ci wa gwamnati tuwo a kwarya kuma ya zama dole a dawo daga rakiyar nuna halin ko-in-kula da akeyi don samar wa fannin mafita na dindindin.

Ya ce abin da gwamnan Kaduna yake yi a Kaduna abu ne mai kyau domin babu yadda za ace wai malami ya kasa cin jarabawar abin da zai karantar wa dalibi.

Ya bada labarin wani abokinsa dan Najeriya da ya dawo makarantar firamaren da ya yi a da domin tallafa musu amma abin da ya bashi mamaki shine ya kasa bambamce tsakanin malamai da dalibai saboda lalacewar ilimi da muka fada ciki a kasar nan.

Share.

game da Author