2019: Sharuddan da Atiku zai cika kafin mu ba shi Takara – Walid Jibrin

1

Jam’iyyar PDP ta yi kira ga Atiku Abubakar da ya tsaya ya bi dukkan ka’idojin da jam’iyyar ta gindaya, ba tare da bin wasu hanyoyin asarkala ba idan ya koma a cikin jam’iyyar nan da ‘yan kwanaki kadan.

Shugaban Kwamitin Dattawan Jam’iyyar, Walid Jibrin ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da PREMIUM TMES jiya Lahadi da dare.

Jibrin wanda tsohon Sanata ne daga jihar Nasarawa, ya ce masu zawarcin takarar kujerar shugaban kasa daga PDP sun karu a kwanakin nan. Ya na mai cewa Atiku zai fuskanci ‘yan takara masu yawan gaske.

Ya kara da cewa PDP za ta bukaci Atiku a matsayin sa na tsohon mataimakin shugaban kasa “ya yi biyayya da kuma bin ka’idojin da jam’iyyar PDP ta shimfida. Idan har ya na so mu ba shi takarar shugaban kasa a zaben 2019.

Jibrin ya ce tun daga lokacin da PDP ta ce dan takarar ta daga Arewa zai fito, dukkan wadanda suka fito suka nuna sha’awar su ta tsayawa takara manya ne, gogaggu.

Sule Lamido da Ibrahim Shekarau na daga cikin wadanda suka fito su na neman takarar shugabancin kasa a 2019.

PREMIUM TIMES ta samu tabbacin cewa nan ba da dadewa ba Atiku zai je mazabar sa domin ya yi rajista.

Rajistar da Atiku zai yi, za ta yi daidai da lokacin taron gangamin PDP na kasa da za a yi a ranar 9 Ga Disamba, 2017, a Abuja.

Share.

game da Author