2019: Fadar shugaban kasa ta mai da wa Sule Lamido martani

2

Gwamnatin mai ci ta maida wa Sule lamido martani kan yadda yake sukar yaki da cin hanci da rasahawa da wannan gwamnati ta sa a gaba.

Kakakin fadar shugaban kasa Garba Shehu ya ce Sule Lamido na yin haka ne domin neman suna.

” Yadda tsohon gwamnan ya ke ta yada zantuka a gidajen yada labarai yana kushe ayyukan wannan gwamnati ya na yi ne don neman suna kawai amma ay kowa ya san abin da yayi musamman lokacin da yake gwamnan jihar Jigawa.

” Wannan shi ne fa mutumin da ya kwashe kudin jihar sa ya loda a asusun ajiya na ‘ya’yan sa. Sannan abin kunya a ce wai mutumin da ke da guntun kashe ta ko-ina- ya fito yana irin wadannan maganganu.

Ya ce mai makon kushe ayyukan wannan gwamnati musamman wajen yaki da cin hanci da rashawa, goya mta baya ya kamata ace an yi.

Share.

game da Author