2019: Buhari ya bayyana alamomin sake tsayawa takara

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana alamomin sake tsayawa takara a zaben 2019.

Ya yi wannan karin hasken ne a babban birnin Cote d’Ivoire, Abidjan a inda ya ke halartar taron hadin guiwa na wasu kasahen Turai da kuma Afrika.

Jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu na cikin ‘yan rakiyar shugaban da kuma gwamnonin Akwa Ibom, Udom Emmanuel da kuma Mohammed Abubakar na Bauchi da sauran tawaga.

Buhari ya halarci wani taron ganawa da ‘yan Najeriya mazauna kasar a makare, a ranar Talata da dare, Buhari ya ce sai da ya jira gwamnonin biyu domin su yi masa rakiya zuwa wurin taron, saboda muhimmancin su.

“Na jira na taho tare da wadannan gwamnonin ne, domin idan za ku ba da labari ga sauran ‘yan Najeriya, ku ka ce musu lokacin da na zo wurin ku, na kawo ziyara, har da wasu gwamnoni na na zo, to hakan ka iya zama silar sake zabe na nan gaba. Na kuma ji dadin da suka samu damar zuwa.”

Buhari na kammala wannan kalami aka barke da dariya ana tafa masa.

NI NA KOWA NE

Buhari ya kara nanata wani kalami da ya yi a ranar 29 Ga Mayu, 2015 a wurin rantsar da shi, inda ya ce shi na kowa ne.

Ya bada misali da cewa shi ne ya sa aka zabi ministan lokacin PDP, Akinkumi Adesina ya zama shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika.

Idan ba a manta ba, jim kadan bayan hawan Buhari kan mulki, ya yi amfani da kusancin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya tura shi wurin shugaban Afrika ta Kudu, Jacob Zuma, ya je ya roke shi domin a bar wa Nijeriya shugabancin Bankin Raya Kasashen Afrika.

Tun da aka kafa bankin cikin 1964, dan Najeriya bai taba shugabancin sa ba, sai wannan karon.

Yayin da ya ke jawabi a wurin taron, Adesina ya ce tattalin arzikin Najeriya kamar ya na aiki ne da jinin Shugaba Buhari.

“Ba da jimawa ba bayan dawowar ka daga hutun jiyya sai tattalin arzikin Najeriya ya rika habbaka.” Inji shi.

Share.

game da Author