Za a yi zaben dan majalisar mazabar Kware/Wammako ranar 28 ga Oktoba

0

A taron masu ruwa da tsaki da aka yi ranar Talata a jihar Sokoto ne kwamishinan zabe na jihar Ibrahim Zarewa ya sanar cewa ranar 28 ga watan Oktoba ne za a gudanar da zaben kujeran dan majalisa na mazabar Kware/Wammako.

Ibrahim Zarewa ya ce INEC za ta gudanar da zaben maye gurbin Ibrahim Muhammed da ya rasu cikin watan Yuli da ya wuce.

Ya kuma yi kira ga jam’iyyu da su tabbatar sun bada sunnan gwaninsu kafin ranar 17 ga watan Oktoba.

Zarewa ya ce duk da cewa sunayen wadanda suka cancanci su yi zabe ya kai 179,032 daga kananan hukumomi biyu din amma ranar zaben wadanda ke da katin zabe ne kawai kada kuri’a ranar zabe.

Share.

game da Author