Za a saki ‘Abu Hassan’

0

Kasaitacciyar fim din nan da kowa ke jira mai suna ‘Abu Hassan’ zai shiga sinima daga ranar 27 ga watan Oktoba a Kano.

Da yake sanar wa PREMIUM TIMES HAUSA, wanda ya shirya fim din Zaharadden Sani ya ce ya gama shiri tsaf domin sakin fim din ranar 27 ga wannan watan.

Sannan ya ce ya shirya irin wannan fim dinne domin ya nuna wa duniya Illar da take cikin irin wadannan ayyuka da yadda iya’ye za su kula da ‘ya’yansu. Ya kuma ce fim din ta nuna yadda jami’an tsaro suma suke arangama da irin wadannan mutane da mabiyansu.

“ Na gama shiri tsaf domin suma nuna fim din Abu Hassan daga ranar 27 ga wannan watan. Sannan za a fara nuna shirin ne a Sinima na shoprite dake Kano.

“ Bayan haka kuma za mu ci gaba da saka shi a sauran jihohin kasar nan. Sannna duk jaruman da suka fito a fim din za a gansu gaba da gaba a wannan rana.”

Abu Hassan dai fim ne da ba Najeriya ba kawai har da kasashen duniya na jiran fitowar wannan fim.

Share.

game da Author