Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya sanar da fara gwajin cutar tarin fuka kyauta a jihar Ogun.
Isaac Adewole ya ce kamar yadda bincike ya nuna mutane 600,000 ke kamuwa da cutar a duniya ko wace shekara.
Ya kuma kara da cewa binciken ya nuna cewa kasashen Afrika sun fi fama da cutar domin cikin mutane shida biyar na dauke da cutar.
Isaac Adewole ya ce saboda hakan ne ya sa gwamantin tarayya ta dauki matakan kawar da cutar ta hanyar zuba kayayyakin gwaji domin yi wa mutanen da ke bukata gwajin cutar kyauta.
” Gwajin na daukan awowi biyu ne kawai sannan kuma ana iya gane ko wanda baya jin magani ne ko mai jin magani ne.”
Discussion about this post