Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya sanar cewa za a gama gina asibitin kula da masu dauke da cutar daji na kasa a Abuja a watan Disemba.
Adewole ya fadi hakan ne a taron wayar da kan mutane kan cutar wanda gidauniyar ‘Cancer Education and Advocacy Foundation of Nigeria, CEAFON’ ta shirya a Abuja inda ya kara da cewa yaduwar cutar daji a Najeriya na neman ya zama ruwan dare Kuma hakan ya sa dole a hana yaduwar cutar ta hanyar samar da wuri na musamman da mutanen da ke dauke da cutar za su rinka samun kula.
Ya kuma kara da cewa gwamantin tarayya za ta gyara asibitocin kula da mutanen dake dauke da cutar guda 8 a fadin kasar nan sannan biyu da ga cikin su za su kammala gyara su kafin wannan shekara ta kare.
Cikin ma’aikatan kiwon lafiyan da suka halarci taron sun shawarci gwamnatin tarayya da ta nemi wasu hanyoyin samar wa asibitotin kudaden da za su dunga amfani da su.