‘Yan sandan sun yi zanga-zangar rashin biyan su albashi

0

Jami’an’yan sandan jihar Kaduna sun yi zanga-zangar lumana a barikin su dake Kaduna saboda rashin samun albashinsu na watanni biyu.

Rashin biyan albashin ‘yan sandan ba na Kaduna bane kawai ya shafa, har da na Jihohin, Kebbi, Gombe, Nasarawa, Ekiti ,Bayelsa, Imo da Ogun.

‘Yan sandan sun yi cincirundo ne a ofishin da ake biyan su albashi domin nuna fushinsu ga rashin albashi.

Wani daga cikin Yan sandan ya shaida wa wannan gidan jarida Premium Times cewa wahala ta ishe su haka ne. Sannan Kuma suna zargi ministan kudi Kemi Adeosun da kin wadata ‘Yan sandan da albashinsu da gangar.

” Yaya za ace wai ana yaki da cin hanci amma Kuma ana kasa biyan ‘,yan sanda.”

Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya ce abinda ‘yan sandan suka yi bai dace ba Kuma hakan tawaye ne.

Share.

game da Author