Jami’an ‘yan sanda a jihar Filato sun dakile wani hari da aka kai kauyen Rotsu, dake kusa da Nkyie-Doghwi a jihar.
“ Wasu mahara ne suka kai wa kauyen hari inda suka kona gidaje uku amma kafin abin ya fi haka jami’an ‘yansanda sun isa garin.”
Kakakin ‘Yan sandan ya ce Allah ya basu nasaran dakile harin ne bayan shigan gaggawa da jami’ansu sukayi gari.
Ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar ya kara aikawa da ‘wasu jami’an ‘yan sandan ko ta kwana garuruwan da ake zaman dar-dar din.