‘Yan majalisa 2 sun koma APC daga PDP

0

Wasu ‘yan majalisan wakilai guda biyu daga jam’iyyar PDP sun cansa sheka zuwa jam’iyyar APC saboda matsalolin da jam’iyoyinsu ke fama da su a jihohinsu.

‘Yan majalisan wakilan da suka canza shekan sun hada da Zephaniah Jisalo wanda ke wakiltan mazabar AMAC/Bwari da Yusuf Tijjani wanda ke wakiltan mazabar Okene/Ogori-Magogo sun sanar da hakan bayan wasikar da kowanen su ya aika wa kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara.

Bayan Dogara ya karanta wasikun shugaba mai tsawatawa na marasa rinjaye na majalisan Umar Barde ya kwabi canza shekan da suka yi.

“Bisa ga dokan kasa a sashe na 68 ya nuna cewa duk dan majalisan da ya canza sheka saboda matsalolin da jam’iyyar sa ke dashi zai sauka daga kujeransa’’.

Kakakin Majalaisar yayi watsi da wannan kira inda ya ce kotu ce kadai za ta iya fayyace irin wannan badakala ba wai da kira haka ba da Umar Barde yayi.

Share.

game da Author