‘Yan bindiga sun bindige tsohon sakataren gwamnatin jihar Filato

0

Shugaban rundunar ‘Yan sandan jihar Filato Terna Tyopev ya ce ranar Talata da yamma wasu ‘yan bindiga sun harbe tsohon sakataren gwamantin jihar Moses Gwom.

Ya sanar da hakan ne wa gidan jaridar PREMIUM TIMES ta wayan tarho ranar Laraba.

Ya ce an kashe Moses Gwam a gidan sa ne dake kusa da shingen binciken shige da fice na STF dake Barikin Ladi sannan mutane 12 sun sami raunuka sanadiyyar harin da ‘yan bindigan suka kai.

Terna Tyopev ya ce wasu mazauna unguwan sun bayyana musu cewa sai da ‘yan bindigan suka hari jami’an tsaron dake shingen binciken shige da ficen STF kafin suka karisa zuwa gidan Moses Gwom.

Ya ce babu wanda suka kama amma suna iya kokarin su don yin garkuwa da ‘yan bindiga.

Share.

game da Author