Yadda El-Rufai zai sake lashe kuri’un Kaduna a 2019 – Uba Sani

0

A wannan hira da gidan jaridar PREMIUM TIMES tayi da tsohon mai ba shugaban kasa Olusegun Obasanjo shawara kuma mai ba gwamnana Kaduna Nasiru EL-Rufai shawara kan Harkar siyasa Mal. Uba Sani ya ce jam’iyyar APC ce za ta sake cin zaben Kaduna a 2019. Bayan haka kuma ya yi bayani akan barakar da ke jam’iyyar a jihar da kuma ko shin zai yi takarar Sanata ko A’a.

PT: Jam’iyyar APC ta rabu kasha uku a Kaduna, Akwai APC wadda kake ciki, akwai APC akida sannan akwai APC Restoration. A matsayinka na mai ba gwamnan Kaduna shawara akan harkar siyasa, kana ganin hakan ba gazawa bace?

Uba: A matsayina na mai ba gwamna shawara akan harkar siyasa, wadannan maganganu da akeyi ba haka bane, rurutasu kawai akeyi. Dama can dole ne a siyasa a sami rashin jituwa sai dai ba kamar yadda ake yayadawa ba. Wasu sun fusata tun bayan zaben 2015, suka yi ta korafin cewa gwamnati ba tayi da su. Dalilin haka ne ya sa wasu suka yi ta yada zantuka. Amma ka sani cewa gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ba mutum bane mai wannan abokinane ko kuma a’a. shi mutum ne mai son ayi abu daidai yadda ya kamata domin Jama’a.

PT: Ba ka ganin wannan rikicin zai iya zama muku matsala ganin cewa zaben 2019 ya fara gabatowa?

Uba: Inaa, bama tsoron komai domin abubuwan da muke yi a Kaduna shine shaidar mu. Da mu ka zo mun sami matsaloli da dama a jihar musamman a fannonin kiwon Lafiya, Ilimi da dai sauran su. Da ga nan ne fa muka harzuka, muka dukufa kuma muka mai da hankali domin ganin mun dawo wa Kaduna da martaban ta a idanuwar mutanen jihar da kasa baki daya. Kamar yadda na fadi, bamu da matsala da ‘yan siyasan Kaduna saboda haka ba ma tsoron komai.

PT: Wasu yan siyasa sun koka cewa wai kunyi amfani da su kun ci zabe, bayan haka kuma kuka yi watsi da su kuka dauko wadanda ba’a ma san su ba kuka nada mukamai a jihar, Me za kace akan haka?

Uba: Wannan Magana ba daidai bane. Duk wanda yayi wa jam’iyya aiki musamman a Kaduna, an yi masa wani abu. Wasu da yawa ba a yi su kowa ya sani bane. Bayan haka kuma gwaman El-Rufai ya nemi duk ‘yan siyasan da suka yi masa aiki a lokacin da su aiko da sunayen wadanda za a nada mukamai. Da yawa da aka turo basu da kwarewa da ilimi akan abbaben da ake bukatan a nada su. Dalilin haka ne ya sa gwamna yanemo da kansa wadanda ya amince da kwarewar su sannan masu mallakin shaidar karatu da ke da karfin da zasu iya hakan ya nada.

PT: Kana ganin El-Rufai na yin abin da ya kamata a Kaduna?

Uba: Kwarai da gaske kuwa, domin abubuwan da muke yi shine jarin mu. Ko in aka shiga a Kaduna ana aiki wanda shine mutane ke son gani, Kuma da haka ne muka karbu. Bama shakka.

PT: Game da shirin sallaman Malamai da gwamnatin jihar ke shirin yi, menene zaka ce akan haka?

Uba: Zamu yi haka ne domin gyara makarantun gwamnati a jihar. Yaya za a ce malamin da ke karantar da dan Aji shida a bashi tambayoyin ‘yan aji hudu ya kasa amsawa kuma ace wai a barshi. Ba ana haka bane don a muzguna wa malaman jihar. Ana yi ne don a gyara makarantun da aikin malumta a jihar. Bayan Haka kuma gwamnatin jihar ta yi wa fannin ilimin jihar shiri na musamman domin inganta ilimi a jihar wajen samar mata ta kaso mai tsoka a kasafin kudin jihar.

PT: Me zaka ce a kan rusa gidan wani dan jam’iyya da gwamna yayi a Kaduna?

Uba: Gwamnan Jihar Kaduna bai rusa gidan kowa ba haka kawai. Hukumar KASUPDA ce ta kawo kukan ire-iren wadannan gidaje a Kaduna bayan haka kuma suka rusa su. Amma ba wai suna zabi bane. An yi haka a duk inda aka ga ba a bi doka ba wajen gina su ko mallakar su.

PT: Kana ganin za ku iya cin zabe a 2019 kuwa?

Uba: Kwarai da gaske, kashi 80 na mutanen karkara na farinciki da ayyukan da muke yi a jihar Kaduna. Da wannan kawai muna da cikakken yakini cewa 2019 na mu ne ba haufi a kai.

PT: Me za kace kan korafin da ake yi wai gwamnan ya handame kudin ‘Paris Club’?

Uba: El-Rufai ya yi fama da irin wadannan hayagaga. An kai shi kara har tsawon shekaru 6 a baya amma kotu ba ta taba kama shi da laifi ko daya ba. Duk wanda yake da wani abu akan gwamna El-Ruafi to shima ya garzaya kotu.

PT: Da gaske ne zaka fito takaran Sanata a Kaduna?

Uba: Yanzu dai ba zan ce eh ko a’a ba. Abin da ke gabana yanzu shine mai da hankali wajen ganin gwamna Nasir El-Rufai ya samu nasara a abin da ya sa a gaba a Kaduna.

PT: Mutane na cewa gwamnati na muzguna wa Sanata Shehu Sani ne don Kana so kayi takaran Kujeran da yake kai, Shin da gaske ne?

Uba: Kamar yadda na fadi maka a baya, Ban ce zan yi takaran kujeran sanata ba yanzu Idan lokaci yayi zan sanar maka koma menene.

Karanta na hirar a shafin mu na turanci: INTERVIEW: Why El-Rufai will win again in 2019 – Uba Sani

Share.

game da Author