Bayanai da muka samu zuwa yanzu sun nuna cewa sojoji 11 Boko Haram suka kashe a wata harin kwantar bauna da suka kai wa sojojin Najeriya a kauyen Sasawa, dake jihar Yobe.
Bayan haka Kuma Boko Haram sun kwace makamai da abincin da sojojin suke dauke da su.
Irin wadannan hare hare sun fara Zama ruwan dare a wasu yankunan jihar Yobe da Barno a dan kwanakin nan.
Kwanakin baya, irin haka ya auku ga wasu sojojin Najeriya ta irin wannan hari na kwantar bauna inda wasu sojoji hudu suka rasa rayukan su.