WHO za ta yi wa yara 300,000 alluran rigakafi a jihar Barno

0

Kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce za ta yi wa mutane 300,000 alluran rigakafin cutar kwalara a jihar Borno.

Kungiyar ta ce za ta hada guiwa da sauran kungiyoyin kiwon lafiya da ta hada kawance da su don gudanar da alluran.

Wuraren da za a gudanar da alluran rigakafin sun hada da sansanoni da kauyukan Damasak, Banki, Bama, Gamburu, Ngala da Pulk dake jihar.

Kungiyar ta ce hakan zai taimaka wajen kawar da cutar musamman yadda bincike ya nuna cewa mutane 4,360 sun kamu da cutar kuma wasu 60 sun rasa rayukan su sanadiyyar kamuwa da cutar a watan Satumba da ya gabata.

Share.

game da Author