Wata mahajjaciya daga jihar Bauchi ta makale a kasar Saudi saboda batar da fasfo dinta da tayi.
Mahajjaciyar wanda daga karamar hukumar Tarawa Balewa ta fito ta na nan a kasar inda jami’ai ke kokarin yi mata sabon fasfo domin ta samu ta dawo gida.
Jami’an hukumar Alhazai na jihar Bauchi sun ce da zaran an kammala yi mata sabon fasfo za ta dawo kasa Najeriya.
Discussion about this post