Wasu ‘yan Boko Haram sun mika wuya a Maiduguri

0

Shugaban jami’an tsaro na Civil Defence NSCDC na jihar Borno, Ibrahim Abdullahi ya ce wasu ‘yan Boko Haram da suka kai 40 sun mika wuya.

Ya sanar da hakan ne da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Maiduguri.

Ibrahim Abdullahi ya kara da cewa cikin watan da ya gabata wasu ‘yan Boko Haram 6 sun mika wuya.

Bayan haka Abdullahi ya ce sun tattauna da masu unguwanin kauyukan jihar da shugabanin addini don karfafa tsaro a yankunan.

Share.

game da Author