Wacce ta fi kowa kiba a duniya Eman Abd El Aty ta rasu a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa UAE.
Kwanakin baya anyi wa Eman Abd El Aty yar shekara 37 wanda nauyinta ya kai kg 500 fida a wani asibiti da ke Mumbai kasar India.
Bayan fidan Eman Abd El Aty ta ragu daga kg 500 zuwa kg 300 amma duk da hakan bata gamsu ba wanda hakan ya sa likitocin suka aika da ita kasar UAE domin sake yi mata aiki.
Ta rasu dalilin daina aiki da zuciyar da kodanta suka yi.