Tunda Kotu bata kama maina da laifi ba, ba daidai bane a kore shi – Cewar Mai taimakawa Buhari

0

Mai taimakawa shugaban kasa kan binciken masu laifi Okoi Obono-Obla ya ce bai ga dalilin da zai sa mutane su yi ta korafe- korafe kan Abdulrasheed Maina ba musamman ganin cewa kotu bata kama shi da laifin komai ba.

Ministan Shari’a da na harkokin cikin gida Abubakar Malami na daga cikin wadanda ke da hannu dumu-dumu wajen maido da Abdulrasheed Maina aiki ta bayan fage.

Ya ce idan jami’an tsaro ko kuma hukumar EFCC ta sanar cewa tana neman mutum ruwa a jallo hakan bai mai da shi mai laifi ba sai kotu ta kama shi da laifi.

Ya kuma ce doka ba ta ba shugaban kasa damar hukunta wani ma’aikacin gwamnati da hukumar FCSC ke da iko da shi ba ko da an kama shi da laifi domin akwai hukumar da wannan nauyin ya rataya a kan sa.

” Idan wani ma’aikaci ya yi laifi hukumar FCSC ke da damar daukar mataki akai. Ko ta dakatar da shi daga aikin sa, ta kuma biya shi rabin albashi sannan ta iya kai shi kotu idan hakan ya taso.”

Da PREMIUM TIMES ta tambayi Obono-Obla game da sa wa a kore shi da da Buhari ya sa ayi, ya ce shida i yan kan bakan sa na har yanzu ba a kama Maina da laifi ba.

” A matsayi na na lauya bai kamata na shiga ayarin mutanen dake cewa Maina na da laifi ba tun da har yanzu Kotu bata kama shi da laifi ba sai dai bawai ina ja da umarnin da shugaban kasa ya bada ba na a kori Maina ba.

Share.

game da Author