TSAKANIN KACHIKWU DA BARU: Kachikwu ya Fasa Kwai

0

Ministan Albarkatun Man Fetur, Ibe Kachikwu, ya bayyana cewa tonon sililin da aka yi wa wasikar da ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari, abin assha da takaici ne. Kachikwu dai ya, rubuta wasikar wadda a ciki ya bayyana irin harkallar kwangilolin dimbin kudade da Babban Manajan Daraktan NNPC, Maikanti Baru ke yi, ba bisa ka’ida ba.

Kachikwu ya ce wasikar wacce aka rika yamadidi da ita a shafukan soshiyal midiya, a yau Talata, ta na daya daga cikin irin rahotanni da ya ke tura wa Shugaban Kasa a kai a kai dangane da yadda ayyuka ke gudana a karkashin hukumomin da ma’aikatun da ke karkashin sa.

Ministan ya nuna takaicin fallasa wasikar, ta bakin kakakin yada labaran Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur, Idan Alibi.

Alibi ya ce an aika wa Shugaban Kasa wasikar ce, ba don a yi wa Maikanti Baru wani zagon kasa ba. Sai don kawai a kara inganta yadda tafarkin da ake gudanar da fahimtar juna da kuma baje komai a kan faifai, ba tare da nuku-nuku ba. Yin hakan ne ya ce zai sa masu zuba jari za su kara amanna da Najeriya.

Wannan bayani ya fito ne sa’o’i kadan bayan fallasa wata wasika da Kachikwu ya aika wa Shugaban Kasa, a ranar 30 Ga Augusta, 2017.

PREMIUM TIMES ta buga rahoton abin da wasikar mai shafi uku ta kunsa, inda Kachikwu ya fallasa yadda Baru ke dibga harkalla da barankyankyamar kwangiloli ba tare da bin ka’idoji ba.

Kachikwu ya kuma roki Shugaba Buhari da ya gaggauta taka wa Baru burki.

Ministan ya ce Baru ya yi wasu canje-canjen son kan sa a NNPC, ba tare da tuntubar Hukumar Gudanarwar Kamfanin ba, ballantana kuma Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur.

Kachikwu dai shi ne Shugaban Hukumar Gudanarwar NNPC.

A cikin wasikar, Kachikwu ya ce Baru shugaban NNPC ya raina shi, kuma ya dauke shi wani “biri-boko.” Ya kuma ce duk wani kokarin da ya yi domin ganawa da shugaban kasa ido-da-ido domin ya bayyana masa harigidon da Maikanti Baru ke yi, bai samu nasara ba.

Canje-canjen da Maikanti ya yi ranar 29 Ga Augusta, na ma’aikata har 55, na daya daga cikin koke-koken.

A martanin da Kachikwu ya yi a yau bayan fallasa wasikar sa, ya ce Shugaba Buhari ya goyi bayan duk wasu gyare-gyare da shi Kachikwu din ya kamata ya yi a NNPC domin a saisaita targaden da Maikanti ya yi wa Hukumar.

Sai dai kuma bai ce ko Shugaban Kasa ya dauki wani mataki kan Maikanti ba, makonni biyar bayan aika wa Buhari wasikar.

Kafin fallasa wasikar a yau, Kachikwu da Baru sun boye sabanin da ke tsakanin su, amma ta-ciki-na-ciki. Sai dai kuma tun cikin shekarar da ta gabata an tabbatar da cewa su biyun zaman ‘yan marina su ke yi.

A baya Kachukwu rashin jituwa ya shiga tsakanin sa da Maikanti dangane da wani aiki a Neja Delta tun cikin 2015.

Haka nan kuma Kachikwu da Ministan Sufuri Rotimi Amaechi sun taba saka kafar wando daya a cikin 2016. Batun kammala Jami’ar Maritime University ce a Jihar Delta ya kai su ga zazzare wa juna jajayen idanu.

Rikicin Kachikwu da Maikanti ya kara bayyana rikin karankatakaliyar da ke furuwa tsakanin na hannun damar cikin gwamnatin Buhari.

Cikin Yuli, 2017 an yi tonon silili tsakanin Ministan Kiwon Lafiya, Isaac Adebowole da shuhaban Hukumar Inshorar Lafiyar ta kasa NHIS, Usman Yusuf, wanda aka dakatar.

Kafin sannan, Ministan Shari’a ya kwashi ‘yan kallo shi da Shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu. Malami ya zargi Magu da cewa ya daina zuwa ya na kai masa rahotannin ayyukan da ya ke yi.

Share.

game da Author