TAMBAYA: Ranar tashin kiyama yadda mutum ya mutu ne zai tashi, tsoho ya tashi tsoho, yaro ya tashi yaro, koko kowa zai tashi a girma daya ne?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Ranar kiyama za’a tashi mutane akan yanayi daban-daban kamar haka:
1 – Mutane duk za su tashi kamar yadda Allah ya haliccesu: tsirara, ba tare da ko kaciya ba, kamar yadda aka haife su. Kowa zai tashi dajikin sa, da siffan sa, da surar sa kamar yadda yake a duniya. Bugu da kari kuma koya za’a tasheshi dan shekara talatin da uka. Shin ya mutu yana tsoho ne, ko yaro ne, ko jariri ne, ko matashi ne, ko dattijo ne, kai koma barinsa ma-haifiyar sa tayi, Allah zai tashe sa dan shekara 33.
Kamar yadda Imam Baihaqi ruwaito a Hadisi Hassan.
2 – ‘Yan Al-jana za’a tashesu da tsayin zira’i sittin , fadin zira’i bakwai, kyawawa, masua hasken faska, kuma duk ‘yan shekaro 33. Duk mai wata tawaya ko nakasu ko nakasa, daga cikin ‘yan Al-janna, Allah zai tada shi sumul, mai cikkakiyar kamala, kyakkyawar sura da siffa, cikin halitar Baban mu Annabi Adamu (AS).
3 – ‘Yan wuta za su tashi cikin mumunan yanayi, gunduma-gunduma, kamarduwastu, masu bakaken fuska, da girman jiki, kamar dutsen Uhudu.
4 – Mutum zai tashi ranar kiyama acikin abinda ya mutu akan sa: idan bawa ya mutu yayin sujada, to Allah zai tasheshi a halin sujada, idan mutum yamutu acikin sabon Allah, to acikin sabon za’a tasheshi. A karkashin haka ne fa hadisan sun zo cewa:
i. Mahajjacin da ya mutu acikin aikin hajji, to za’a ta sheshi yana TALBIYA: Labaikal Lahumma Labbaik…
ii. Mujahidi da ya mutu a filin daga, to za’a tasheshi jina-jina.
Rauninsa launin jini amma kanshin sa kanshin al-miski.
iii. Mai satan kayan ganima da sauran musu sata ko cin amana, za’a tashesu dauke da abinda suka sata yana kuka ko kara irin nasa. Misali: in motace tana kukan mota, akuya tana kukan akuye…yana dakon kayan
tsiyar sa niqi-niqi.
iv. Ma-ciyin riba, zai tashi, yana marisa da maye kamar bugagge ko mai ciwon farfadiya.
v. Azzalumin shugaba zai tashi an kafamasa tuta ta zalunci, gwargwadon girman zaluncin sa.
vi. Ladan zai tashi da tsawon wuya na al-hairi.
vii. Azzalumin miji da ke nuna fifiko tskanin matan sa, zai tashi da bangaren jikinsa a shanye, wato paralysis.
viii. Wanda ya kashe kansa, zai tashi yana caccakawa kansa makamin da yayi amfani da shi don kashe kansa.
ix. Wanda ya juwa bayansa daga ayoyen Allah, ya ki imani da biyayya, to Allah zai tasheshi makaho, kamar yadda ya rintse idon sa daga ganin gaskiya.
x. Mai girman kai za’a tasheshi kamar girma kiyashi, kumai a ranar kiyama ya fishi girma.
Ya Allah! ka tsaremana Imaninmu da Mutuncinmu kuma ka azurtamu da ALJANNA. Amin.