TAMBAYA: Mutumin da ya kama wani namiji a gidansa, shin zai iya kiransa kwarto ko kuma ayi masa hukuncin haka

0

TAMBAYA: Mutumin da ya kama wani namiji a gidansa, shin zai iya kiransa kwarto ko kuma ayi masa hukuncin haka

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Ya kai dan uwa mai albarka, Allah ya gafartama ka, mutumin da ya kama wani namiji a gidansa, yana neman matarsa ko yana fasikanci da ita, kotu ce kawai za ta iya tabbatar da kwartancinsa ko rashinsa. Kuma ita ce takeda karfin yenkemasa hukunci ba mai gidan ba .

Wanda ya kama wani yana zina da matar sa, to, zai yi aiki da hukunci kamar haka:

1) Yakafa shaidu hudu da zai gurfanar da su a gaban kotu don zartar musu da hukuncin Haddi. Allah yace acikin suratun Nisa’i aya ta 15 “kuma wadanda suka je ma alfasha daga cikin matanku, to, kunemi shaidar mutane hudu akansu”

2) Yayi LI’ANI, wato yakai kara gaban kotu kuma yayi rantsuwa hudu cewa ya ganta tana zina, ya cike da rantsuwa ta biyar cewa tsinuwar Allah ta tabbata akansa in karya yake mata. Ayoyin farkon suratun Nur sunye cikakken baya ni.

3) Wajibi ne bin doka a musulunci, kuma musulmi bai daukar doka a hannunsa. Amma idan mijin ya dau doka a hannunsa sabo da tsananin kishi, har yakashe kwarton, ko kuma subiyun. Malamai sun ce, idan akwai shedu, to, babu komai akansa. Amma idan babu shaidu, to, za’a yi masa hukuncin kisa.

An karbo daga Abu Huraira, Sa’ad Dan Ubada ya tambayi Annabi: shin indan nasami wani namiji yana fasikanci da matata, sai nakawo shaidu?

Annabi SAW ya ce NA’AM, sai Sa’ad ya ce Ina rantsuwa da wanda ya aikoka da gaskiya, bazan iya saurarawa, sai na sareshi da takobi. Sai Annabi SAW ya ce:

shin kunji abinda shugabanku yake fadi, Lallai shi mai kishi ne, Amma ni nafi shi Tsananin kishi, Kuma Allah Yafi kuwa Tsananin kishi. Kuma duk da tsananin kishinmu, muka ce abi dokar
shaidu ko LI’ANI.

Ya Allah ka tsare mana imaninmu da mutuncinmu. Amin.

Share.

game da Author