TAMBAYA: Menene falalar karanta ya zal-jalali wal-Ikram? يَا ذَا الْجَلالِ وَالإِكْرَامِ

0

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Malamai sun kasa Sunayen Allah zuwa gida biyu: Kashi na farko suna nuna karfin iko na Allah, kashi na biyu kuwa suna nuna cikar kamalarsa. Hakika wannan sunan Allah na “Zul-Jalali Wal-Ikram” ya hada dukkanin bangarorin sunayen Allah baki daya.

Hadisi ya inganta daga acikin riwayar Imamu Ahmad, Annabin Rahma SAW yace: “ ku nace da zikin “Ya Zal-Jalali Wal-Ikram”. Kuma wasu malamai suna da fahimtar cewa “Zul-Jalali Wal-Ikram” shi ne Sunana Allah Mafi Girma, wato Ismul-lahil A’zam.

Allah ya ambaci wannan suna na “Zul-Jalali Wal-Ikram” a Al-Kur’ani ( Suratur-Rahman aya ta 27 da ta 78). Kuma Annabin Tsira SAW yayi addu’a da wannan suna agurare daban-daban. Wannan suna yana cikin zikirin Annabi SAW a bayan kowace Sallah.

Rokon Allah da wannan suna na “Zul-Jalali Wal-Ikram” ya na yaye dukkan damuwa, ya na kwaranye dukkan bakin ciki da rudani, ya na tunkude fitana ba bala’i. bugu da kari kuma ana samun biyan bukata cikin dukkanin bukatar da aka roki Allah da wannan suna. Allah ya na amsawa kuma ya biya bukatar mai bukata.

Ya Zal-Jalali Wal-Ikram muna rokon ka da wannan suna da ka tsaremana Imaninmu da mutuncinmu sannan ka a zurtamu da Al-janna. Amin.

Share.

game da Author