TAMBAYA: Mene ne illar mace ta yi yaji? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Mene ne illar mace ta yi yaji?

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Yaku ‘yan-uwa maza! lallai Allah Ta’ala ya shugabantar daku akan mata, kuma ya umurce su da yi muku biyayya kamar yadda ya umurceku da kyautata musu. Musulunci yayi muku wasici da tausayawa matanku, hakuri dasu, taimaka musu kamar yadda yayi hani da cutatar da su ko muzguna musu a cikin zamanta kewa.

Yaji shine matar aure ta bar gidan mijinta ta koma gidansu ko kuma gidan waliyinta ko magabacinta, domin sabani ko kuma cutarwar mijinta.

Idan matar aure ta fita daga gidan mijinta domin kawo gyara ga aurenta ko neman hakkinta, to, bata sabawa Allah ba. Ko da kuwa ta fita ba izinin mijinta, matukar ta nufi gurin alkali ne, ko waliyanta ko magabatanta ko kuma wani shugaba domin neman hakkinta. Amma wajibe ne ta yi gaggawar komawa gidan mijin ta da zarar ta kai korafinta. In
bata yi gaggawar komawa ba, to, tana cikin sabon Allah.

A musunci ba’ayar da mata ta kauracewa gidan mijinta ba, sai dai idan akwai hadari a gareta cikin zaman gidan. Idan matar aure ta bar gidan mijinta, ba tare da dalili mai karfi ba, to, tana cikin sabon Allah, kuma ta wulakantar da hakkokin mijinta tare da hakkokin Allah da ya shimfida akanta.

Miji zai iya shiga wuta idan ya tuzartar da amanar matarsa, wajibensa ne ya girmamata, ya dau nauyin dukkanin bukatunta, gwargwadon ikonsa. Ya zama irin mutuminan mai hikima, wanda ya samu sabani da matarsa: sai aka tambaye shi musabbabin sabaninsu, sai yace: mijin kwarai baya tona asirin matarsa kuma baya tozartata. Bayan ya saketa, aka kara tambayarsa musabbabin sabaninsu, sai yace: Namiji baya fadin aibin
matar wani.

ILLOLIN YAJI GA MA’AURATA

1) Yaji yana haifar da mutuwar aure ko da kuwa ma’auratan suna so kuma suna kaunar juna.

2) Haifar da gaba tsakanin surukai da dangin ma’aurata ko da kumama’auratan sun manta da abinda ya kowo sabani tsakaninsu.

3) Yana bada kafa ga shaidan da sauran makiya a cikin mutane.

4) Yana haifar da gori, wulakanci, bata sunan zuri’a, surukai da dangin ma’aurata.

5) Yana haifar da kunyata, nadama da kuma da-nasani tare da kaskanci ga ma’auratan.

6) Yana kawo kunci ga ma’aurata ko yalansu da iyayensu.

7) Yaji zai iya shafan rayuwar ‘ya-‘ya ta bagaren tunani, tsoro, rashin yarda da sauran matsalolin da su keda alaka da dan-adamtarkar sa.

8) Yana tona asirin ma’aurata, bayan Allah ya ambaci alakar ma’aurata da alkawali mai karfi, wanda bai kamata wani yaji tsakaninsu ba.

9) Yaji na jefa ma’auta cikin halaka, idan suka ki yima junansu adalci, hakan yana iya sasu su zalunci juna.

10) Yana haifar da girman kai ga ma’aurata, kin daukar laifi ko kuskure tare da jin kai da isa.

Ya Allah! ka zaunar da gidajenmu lafiya, kuma ka yi albarka ga aurarrakinmu da zuri’armu. Amin.

Share.

game da Author