Gwamnatin Tarayya ya saki zunzurutun kudi har naira biliyan 100 domin aikin gina titina har 25 a fadin kasar nan.
An saki kudin ne a karkashin sabon tsarin tasarifin kudi na Musulunci, wato SUKUK. Za a yi ayyukan ne a karkashin Ma’aikatar Ayyuka, Makamashi da Gidaje ta Tarayya.
Ministar Kudi Kemi Adeosun ce ta bayyana haka a yau Alhamis, a Abuja inda kuma ta damka cakin kudin ga Ministan Makamashi, Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola.
Dama dai a cikin watan Satumba sai da gwamnatin tarayya ta saki wasu kudin naira biliyan 100, a karkashin Sukuk, wadanda tun cikin makon da ya gabata aka kammala ayyukan da aka yin su.
Adeosun ta ce irin yadda aka karbi tsarin Sukuk hannu bib-biyu daga gwamnatin tarayya, ya na kara nuna yadda ake amanna da tsarin inganta tattalin arziki na wannan gwamnatin a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari.
Ta ce za a yi amfani da kudin domin a gina nagartattun hanyoyi har guda 25 a dukkan yankuna shida na kasar nan.
Ta kara da cewa titinan za su kara habbaka gudanar da hada-hadar tattalin arziki a fadin kasar nan.
Ta na mai cewa za a kashe naira biliyan 16.67 a kowane yanki.
Za a gina titina 5 a yankin Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Kudu, sannan Arewa ta Gabas, Arewa ta Yamma da Kudu maso Gabas duk za su samu titina hudu kowane.