SHIGA SHARO BA SHANU: Majalisar Tarayyya ta shiga rigimar Kachikwu da Maikanti

0

A Laraba ne Majalisar Tarayya ta kafa kwamitin mambobi 9 domin su binciki zarge-zargen da Ministan Man Fetur, Ibe Kachikwu ya yi wa Shugaban Kamfanin Mai na NNPC, Maikanti Baru.

Majalisar ta kuma umarci kwamitin da ya binciki wasikar da Minista Kachikwu ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya fallasa harkalla da zagon kasar da Baru ke yi masa.

Sanata Aliyu Wammako ne zai binciki kwamitin wanda ya kunshi Tayo Alasoadura, Akpan Bassey, Samuel Anyawu da Ahmed Ogembe. Sauran ‘yan kwamitin sun hada da Rose Oko, Baba Garba da Kabir Marafa.

Da ya ke gabatar da kudirin neman yarda a yi binciken, Sanata Samuel Anyanwu ya jaddada bukatar Majalisar Dattawa da ta binciki irin harkallar da Baru ya yi a batun a kan zargin asarkalar kudi da kamfanin Duke Oil, wanda kamfanin a ta bakin sanatan, ya ce abokin cin mushen kamfanin NNPC ne.

Anyanwu ya ce Duke Oil fa a kasar Panama ya ke da rajista, ba ya biyan haraji a Nijeriya.

Wannan kamfani na Duke Oil, ya na samun dimbin kwangiloli da harkalla da jigilar mai daga NNPC a kasashe daban-daban.

“Majalisar Dattawa na sane da cewa Shugaban NNPC ya na jibga manyan kwangiloli ga Duke Oil, baya ga yadda ya ke ba kamfanin damar lodi da jigilar danyen mai da iskar gas. Hakan ya maida Duke Oil tamkar wata ‘yar-rototuwar da ta tsuguna sai ta rika yi musu kashin kudi kawai.”

Ya kara da cewa irin kwamacalar da ke gudana tsakanin NNPC da Duke Oil, abin dubawa ce a cikin gaggawa.

Sai dai kuma akwai masu ganin cewa Majalisar Dattawa ta yi azarbabin shiga-sharo-ba-shanu, domin wasikar da Kachikwu ya rubuta, ba Majalisar Dattawa ya rubuta wa ba, Shugaban Kasa ya aika wa da ita.

Ana ganin cewa kamata ya yi majalisar dattawa ta fara saurarawa domin ta jira ba’asin da zai fito daga Fadar Shugaban Kasa tukunna.

Share.

game da Author