Shugaban Kungiyar Yarbawa ta Oduduwa Peoples Congress, wato OPC,Gani Adams, ya zama sabon Aare Ona Kakanfo, wadda sarauta ce ta kwamandan rundunanr mayakan Alaafin na Oyo a zamanin da can kafin Mlkin Mallaka.
Alaafin na Oyo, Lamidi Adeyemi ne ya nada shi wannan sarauta a lokacin bikin zagayowar ranar haihuwar sa shekaru 79, jiya Lahadi.
Gani Adams ya gaji hamshakin attajiri, marigayi Mashood Abiola, wanda ya rasu 1998. An bai wa Abiola sarautar Aare Ona Kakanfo cikin 1988.
Discussion about this post