Saraki ya roki duniya ta yi wa ta’addanci taron-dangi

0

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya yi kira ga shugabanni na duniya su hada karfi su yi wa ta’addanci taron dangin da za a yi masa kakkabar-‘ya’yan kadanya, kasancewa yanzu a duniya ta’addanci shi ne babban abokin gabar kowa.

Saraki ya yi wannan jawabi ne lokacin da ya ke ganawa da Mamakin Majalisar Gudanarwar kasar Iran, Ali Larijani, a Taron Kungiyar Shugabannin Majalisu na Duniya, karo na 137 a birnin Petersburg, Rasha, a yau Litinin

Shugaban na Majalisar Dattawa ta kasa ya ce nauyi ne da ya rataya a wuyan shugabannin duniya su ga cewa sun hada kai sun kakkabe ta’addanci a duniya.

“Lokacin da mu ke yara kanana, duniya ba haka ta ke ba wajen yaki da ta’addanci.”

Shi kuwa Larijani ya ce ya ji dadin damar da ya samu har ya gana da Saraki su ka tattauna batutuwan da su ka shafi Iran da Najeriya.

Share.

game da Author