Wata Kungiya na likitoci a Najeriya ta yi kira ga gwamantin tarayya da ta samar da Shirin inshorar lafiya a cibiyoyin kiwon lafiya na fadin kasar nan.
Shugaban kungiyar Femi Dokun-Babalola ya yi kiran inda ya kara da cewa hakan zai bada damar aikawa da mutanen da cutar su ta gagari cibiyoyin kiwon lafiyan zuwa manyan asibitocin kasan.
Ya ce hakan zai rage matsalolin cunkoson da ake samu a mayan asibitocin kasan.