Jakadan Najeriya a kasar Thailand Nuhu Bamalli ya yi kira ga ‘yan Najeria musamman matasa dake fita zuwa kasar Thailand da su tabbata sun bi ta yadda doka ta gindaya domin gujewa karewa a gidan yari.
Ya yi wannan kira ne a taron baje kolin duwatsun lu’u-lu’un da aka yi a Abuja inda ya kara da cewa sama da matasan Najeriya 1000 ne ke kulle a kurkukun kasar Thailand.
” Yadda matasan mu tsare a gidajen kurkukun kasar Thailand abin tashin hankali ne saboda kar ya doka da shiga ba kamar yadda doka ya gindaya.”
Bamalli ya ce Najeriya da Thailand za su ci gaba da gudanar da kasuwancin duwatsu lu’u-lu’u tsakanin kasashen biyu.
Ministan hako ma’adanai Kayode Fayemi ya ce Najeriya na rasa dala biliyan 3 kowace shekara saboda yadda wasu a kasar ke siyar da duwatsun lu’u-lu’un ta hanyoyin da bai kamata ba.