An dai ga yadda rigimar ta kai ga soke kwangilar tara kudaden haraji ta shekara da shekaru da Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa, NPA ta bai wa Intels, kasaitaccen kamfanin nan na Atiku.
BAYAN TIYA AKWAI WATA CACA
Ba wai rashin jituwar da aka rika yayadawa ta kin samun matsaya kan kin amincewar da Intels ya yi a rika tara dukkan tulin kudaden harajin da ya tara a asusu daya, wato TSA ne kadai dalilin kazamcewar rigimar ba.
PREMIUM TIMES ta yi abin da Hausawa ke cewa bin-diddigi, wai kuturta da bin kanwar kishiya. Ta kuma zakulo yadda NPA ta nemi ta sabule wa Intels wando ta ka, da nufin karya kaka-gida da kuma babakeren da kamfanin ya yi shi kadai ya na tara kudin haraji daga kamfaninin da ke hada-hadar fetur da gas ta hanyar jigila a manyan jiragen lodin kaya a cikin teku.
Wannan jarida ta bi kwakwaf inda ta yi nazarin wasu takardun bayanai tun daga 2006, inda ta gano yadda NPA da Intels su ka rika cin karen su ba babbaka, har zuwa lokacin da sabani ya shiga tsakanin hukumar da kamfanin su ka fara ci wa juna kwala.
MUN GAJI DA INTELS
Cikin watan Mayu, Premium Times ta bada labarin yadda NPA ta rubuta wa Ministan Shari’a, Abubakar Malami wasika inda ta roki a soke yarjejeniyar da NPA ta yi da Intels.
RIGIMA KAN ASUSUN AJIYAN KUDI NA BAI DAYA, TSA
Cikin Yuni 2016, NPA ta umarci Intels da cewa ya rika tara dukkan harajin da ya tara da kudaden da za ta biya a cikin asusu daya a Babban Bankin Tarayya, CBN, sannan daga baya sai a raba riba.
Intels ya ce hakan ba zai yiwu ba, domin ya na karbar kudade daga bankunan kasuwanci ya na gudanar da ayyukan tara haraji da kudaden shiga kamar yadda tun farko aka yarda a shirin kwangilar. Don haka idan ya daina tara kudi a bankunan kasuwanci, ba za su rika bai wa Intels lamunin kudaden gudanar da ayyuka ba kenan.
TARUKAN DORA WA JUNA LAIFI
Wannan rashin jituwa da rashin fahimtar juna ta kai ga bangarorin biyu sun rika gudanar da tarukan neman mafita. Amma duk lokacin da ka zauna, akan tashi baram-baram.
An yi wani zama inda Intels ta ce matsala babba a CBN ita ce idan kudi sun shiga, ba a san ranar fitowar su ba. Don haka Intels ‘yan kasuwa ne ba gwamnati ba.
Ganin haka sai NPA ta amince Intels ya rika ajiyar kudade a bankuna uku kacal, tare kuma da CBN. Wannan tayin ma Intels ya ce bankuna uku sun yi masa kadan.
KOKAWA HAR SUKA AFKA FADAR SHUGABAN KASA
Ranar 16 Ga Janairu, 2017, NPA ta rubuta wa shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari da kuma Ministan Shari’a Malami kai har da Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, aka sanar da su kunnen-kashin da Intels ke nunawa wajen bijire wa tsarin ajiyar kudaden haraji a asusu daya tal. Sannan kuma NPA ta nemi shawarar matakin da za ta dauka.
A BI DOKA A ZAUNA LAFIYA
Dukkan bangarorin biyu su ka umarci NPA ta rattaba wa Intels lallai yadda aka ce a yi din nan, to hakan shi kadai ne mafita. Hakan kuwa aka yi. Intels ya ce bai san haka ba, NPA ta ce ‘shege-ka-fasa.’
KARAKAINAR WASIKU
An ci gaba da karakainar wasiku tsakanin juna har ta kai ga ranar 27 Ga Satumba, 2017 Ministan Shari’a ya ce ki dai a bi doka, ko kuma a soke kwangilar. Hakan kuwa aka yi.
SOKE KWANGILA
Ranar 10 Ga Oktoba an rubuta wa Intels wasikar sanar da shi an soke kwangila. Inda shi kuma ya yi barazanar garzayawa kotu. Tare da bayar da kwanaki bakwai a dakatar da soke kwangilar ko kuma NPA ta amshi sammacen alkali.
MAJALISAR DATTAWA TA SHIGA TSAKANI
Cikin wannan makon ne Majalisar Dattawa ta bayar da umarni Ga NPA ta dakatar da soke kwangilar da aka yi wa Intels domin ita majalisar ta yi bincike.
INTELS YA BADA HAKURI
Ranar Laraba da ta gabata ne Intels ta nemi afuwa tare da shan alwashin zai bi umarni da ka’idojin NPA.