Shugaban kamfanin mai na Kasa NNPC, Maikanti Baru ya karyata koken da ministan mai na Kasa Ibe Kachikwu yayi cewa wai kamfanin mai din karkashin jagorancin Maikanti Baru ta buga harkalla a wasu kwangiloli da ma’aikatar ta bada wanda a matsayinsa na ministan mai bashi da masaniya a kai.
A wata doguwar wasika na mai da martani da Baru yayi wanda babban darektan kula da sashen ayyukan yau da kullum da hudda da jama’ a ya fitar Ndu ya ce babu wata sama da fadi da akayi a kamfanin kamar yadda ministan yake ikirarin anyi.
Baru ya ce duk wani abu da suka yi da ya shafi harkar mai a kamfanin sai da suka bi doka sannan suka aiwatar da shi. Babu wani abu da akayi bada sanin duk wanda ya kamata ya sani ba.
Sannan kuma ya karyata cewa da Kachikwu yayi wai ya bada kwangila har na Dala biliyan 25 inda ya ce ko kadan haka bai faru ba. Ya ce aiyukkan da aka bada duk ba aiyuka bane da aka yi musu kudi wai ga abin da za a biya. Ya ce kwangiloli ne da ake bada su cikin yanayin na bin dokar bada su kamar yadda yake.
Ya ce duk abinda ministan ya fadi ba haka bane kuma dalilin kare kansa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurce shi yayi ne ya sa ya fito da wadanna bayanai dalla-dalla.
Karanta labarin a shafin mu na Turanci a nan: www.premiumtimesng.com
Discussion about this post