Olisa Metuh ya roki kotu ta gaiyaci Jonathan ya bayyana a gabanta

0

Tsohon kakakin jam’iyyar PDP, Olisa Metuh ya roki kotu da ta gaiyaci tshohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya bayyana a gabanta domin gabatar da shaida a kan sa.

Olisa Metuh ya fadi hake a kotu da ake ci gaba da sauraron shari’ar sa da akeyi na wasu kudade da shima ya amsa daga kudin makamai da ake tuhumar Sambo Dasuki da yin watanda da su a gwamnatin da ta shude.

Kotu ta bukaci Dasuki ya bayyana a kotun amma hakan bai yiwu ba a zaman ta na yau.

Share.

game da Author