Obasanjo da IBB suke da kaso mafi yawa a ‘Unity Bank’, su suka rada mata suna

0

Tsohon shugaban bankin Unity ‘Unity Bank’ Thomas Etuh ya ce Tsoffin shugabannin kasar nan, Janar Olusegun Obasanjo da Janar Ibrahim Babangida ne suka rada wa bankin Unity suna ‘Unity Bank’ don hadin kan kasa.

Etuh ya ce Obasanjo da Babangida sun yi haka ne a lokacin ganin cewa bankuna kusan 9 ne suka hadu suka kafa bankin da kuma kishi da hadin kan kasa.

Bankunan sun hada sa Bank of the North, Tropical Commercial Bank, Intercity Bank, African Merchant Bank, First Interstate Bank, New Nigerian Bank da Societe General Bank.

Ya kara da cewa dalilin zuba jari a bankin da suka yi yanzu bankin yana iya alafahari da da jarin da yake dashi da yakai har naira Biliyan 80.

Babangida da Obasanjo ne suke da kaso mafi yawa a hannun jarin bankin.

Share.

game da Author