Ni da siyasa har abada, inji Obasanjo

0

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa ya bar harkokin siyasa har abada, tare da cewa akwai bukatar a kasar nan a samu jam’iyya mai mulki mai karfin gaske, kuma a samu jam’iyyar adawa mai karfi ita ma, ta yadda dimokradiyya za ta inganta.

Obasanjo ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke zantawa da wasu ‘yan jaridu, jim kadan bayan ganawar da Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar PDP, yau a Abeakuta, jihar Ogun.

Tsohon shugaban ya kara jaddadawa lallai ya yi bankwana da siyasa, sai dai ya kara bada hasken cewa amma fa wannan mataki da ya dauka, ba ya na nufin ya daina bayyana ra’ayin sa kan kishin kasar sa ba.

“Na fada a baya, kuma yanzu ma zan sake fada cewa ni da harkokin siyasa faufaufau. Amma zan rika shiga sabgogin duk da suka shafi ci gaban kasar nan.” Inji Obasanjo.

Dangane da ganawar da ya yi da Makarfi kuwa, Obasanjo ya ce wannan kuma batu ne na mutane ko abokai biyu – lokacin da na ke shugaban kasa, shi kuma Makarfi ya na gwamnan jihar Kaduna. Inji shi.

Share.

game da Author