Kungiyar Kwadugo a jihar Kaduna ta karyata cewa da gwamnan jihar yayi wai sama da kashi 66 bisa 100 na malaman firamaren jihar basu iya cin jarabawar yan Aji hudu da gwamnatin jihar ta shirya musu.
Shugaban kungiyar, Adamu Ango ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa gwamnan ya fitar da duka sakamakon jarabawar da ya yi wa malaman sannan ya fadi ko an bi yadda atsarin shirya jarabawa na gwajin malamai da aka amince dashi a duniya.
Ango wanda shine Sakataren kungiyar malamai NUT, ya ce a gaskiya gwamna El-Rufai bai kyata wa malamai ba da ya tozarta a filin Allah Ta’ala.
Yayi wa gwamna EL-Rufai tambayar cewa idan gaskiya ce gwamnatin jihar take kan maganar malaman, Ina sakamakon jarabawar da malaman suka rubuta domin wannan shine karo na uku da ake rubuta irin wannan jarabawa? Da wani tsari aka shirya jarabawar sannan wace hukuma ce ta shirya sannan da sauransu ganin cewa har yanzu gwamnatin bata gama tantance malaman makarantun ba.
Ya ce babu dalilin shirya wa malamai wata jarabawa bayan ba gwamnati bane za tayi haka. Akwai hukuma ta musamman dake shirya wa malamai irin wannan jarabawa. wanna ba huruminsa bane. Kamar yadda Ango yace.
Ango ya kara da cewa abinda gwamnati za ta iya shine ta tura malaman karo ilimi da wayar mus da kai ta hanyar shirya tarorruka kan sanin makamashin aiki da bunkasa hanyoyin karantarwa amma ba wai ta shiga sharon da ba nata ba.
Sannan ya karyarta cewa da gwamnan yayi wai zai dibi sabbin ma’aikata 25,000 bayan ya sallami 20, 000 cewa shigo-shigo ba zurfi ne suke so suyi ta hanyar shirya jarabawar amma tabbas dama can suna so su kori malaman firamare din.
Discussion about this post