Ndume ya karyata kazafin Mari da majalisar Barno ke yi masa

0

Sanata Ali Ndume ya karyata zargin da aka yi masa cewa wai ya sharara ma mari wani dan majalisar dokokin jihar Barno mai suna Bukar Daja-Ali wanda ke wakiltan Damboa.

Majalisar dokokin jihar Barno ta zargi Ndume da marin Bukar Daja-Ali a taron siyasa a Maiduguri.

Ali Ndume ya ce kwatakwata bai taba haduwada wani dan majalisa mai suna Bukar Daja-Ali ba. Ya ce zai iya tunawa wasu tsagera sun zo gidan sa suna neman tada hankalin iyalan sa da shi kan sa. ” Da na fito domin in samu dalilin yin haka sai wani dan majalisa da ya zo tare dasu ya shiga gabana. Ban ce masa komai ba domin har ya nemi ya ture ni amma duk da haka kyale shi na wucewa ta. Ban san inda maganar mari ya fito ba da ake ta yayadawa har majalisar jiha na yanke hukunci a kai.”

Ndume ya ce kazafi ce kawai don a ci masa mutunci da kuma bata masa suna.

Ya kalubalanci Daja-Ali da duk wani mai mara masa baya a majalisar da ya kawo shaidun da zai nuna ya mari dan majalisar.

Majalisar jihar dai ta ce ba za at sake zama a zauren ta ba sai an bi ma Daja-Ali hakkin sa.

Share.

game da Author