Zai yi wuya a ce ga jihohi 10, 15, 8 ko biyar da su ka fi lalacewa a fannin samar da ingantaccen ilimi a kasar nan.
Amma kuma tabbasa idan za a yi lissafin, to kusan 15 din duk daga Arewa su ke. Sai dai kawai da wuya a ce ga karshe a wani matakin.
Dalili kuwa shi ne, ba da ma’auni daya ake suna nagarta, kwazo, kulawa da kuma samar da ingantaccen ilimi ba.
Yayin da Hukumar Daukar Malaman Makaranta ta Najeriya ke auna nagartar ilmi ta hanyar kwararrun malamai, ita kuwa WAEC ta na auna wa ne da yawan daliban da su ka ci jarabawar kammala sakandare.
Yayin da UBEC da SUBEC ke auna nagartar ilimi a jiha ta ma’aunin samarwa da wadata makarantun firamare da kayan koyon karatu da suka hada har da samar da ajujuwa, ita kuma JAMB ta na auna nauyin nagartar ilmi a jihohi ta yawan daliban da su ka ci jarabawar shiga Jami’o’in kasar nan.
SABUBBA 10 DA SU KA DURKUSAR DA ILMI A AREWA:
1. BOKO HARAM: Cikin makon jiya shugaban Hukumar Daukar Malamai ta Kasa, Josia Ajiboye, ya ce Boko Haram sun kashe malamai har 611 a Arewa maso Gabas, daga 2009 zuwa yau
Sannan malamai 19,000 sun rasa muhallin su duk sanadiyyar harin Boko Haram.
Dubban yara sun zama marayu ta yadda karatun ya gagare su.
Dubban iyaye matan da aka kashe mazan su, ba su da karfin daukar nauyin yaran da su ka kasa ci gaba da zuwa makaranta.
2.SIYASA: Siyasa na daya daga cikin musabbabin lalacewar ilimi a Arewa. A nan ana maganar yadda gwamnoni da ‘yan siyasa ke shigar-kutse a harkar ilmi ana daukar malaman da akasarain su dakikai ne, su na koyarwa a makarantu. Ana yin haka nan don a saka musu ladar wahalar yakin neman zabe.
3. DAKIKAN MALAMAI: Wannan matsala ce mai zaman kan ta. Kuma laifin hukumomin ilimi na jiha da kananan hukumoni ne.
A makon da ya wuce an bayyana cewa akwai dakikan malamai har 300, 000 a Najeriya.
Jihar Kano ce a sahun gaba wajen yawan dakikan malamai har 25,000.
A kididdigar 2010, akwai dakikan malamai 2017,818. Amma sai ga shi ya zuwa yau 2017, bayan shekaru bakwai, sai ma kari aka samu zuwa dakikan malamai 300,000.
A kididdigar 2010, jihar Adamawa na da dakikan malamai 6,231.
4. RASHAWA DA CIN HANCI: Su ma sabubba ne na lalacewar ilmi, ta yadda manan jami’an gwamnati ke karkatar da makudan kudaden da ya kamata a inganta harkar ilmi da su. Ko kuma a aiwatar da ayyuka marasa inganci bayan an ware makudan kudaden da ya kamata a yi nagartaccen aiki.
5. RASHIN MALAMAI MASU KISHI: Malamai da yawa babu kishin bayar da ilmi a kan su har ma a zuciyar su.
Yawancin malamai ba au zuwa makaranta kan lokaci. Wasu ma sai ranar biyar albashi ake ganin su.
Malamai da yawa su na sakin aikin koyarwa su tafi kabukabu da babur din achaba ko Keke NAPEP. Da yawa na tafiya kwadago a lokacin da ake darasi a ajujuwan su.
6. RASHIN KULA DA MALAMAI: Jihohi da yawa ba su biyar albashi sai an nemi a ba hammata iska. Jihohi da yawa kuma ba su damu da sauran hakkokin malaman makaranta ba.
Ana samun matsala wajen karin girma ko karin mataki ga malamai.
7. MALAMAN BOGI: Jihohi da yawa na fama da matsalar malaman bogi. Ga dai sunan malami a takardar sunayen masu karbar albashi, amma babu malamain, kuma ba a san mai karbar albashin nasa ba.
A kananan hukumomi sau da yawa shugaban karamar hukuma na da nasa sunayen na bogi, haka mataimakin sa. Shi ma shugaban Jam’iyya har ma da hakimi duk su na karbar albashin sunayen bogin da su ka dafkara ana karbe albashin.
8: MAKARANTU MASU ZAMAN KAN SU: Su ma babbar matsala ce ga makarantu na gwamnati. Yadda ake bayar da karatu a makarantu masu zaman kan su, ya sha babban da makarantu na gwamnati.
Dalili kenan ba a ganin kokarin dalibin da ya gama firamare ko sakandare ta gwamnati.
Sai dai kawai za a iya cewa makarantu masu zaman kan su akwai tsada. Amma kuma dama Bahaushe ya ce: ‘daidai kudin ka, daidai shagalin ka.’
9. WATSI DA MAKARANTUN GWAMNATI: A yau tun daga kansilan karamar hukuma har shugaban kasa babu wanda dan sa ke makarantar gwamnati.
Babu ‘ya’yan ministan ilmi, babu ‘yar gidan kwamishinan ilmi ko wani darakta ko Sakataren ilmi. Kowa ya tura ‘ya’yan sa makarantu masu zaman kan su, inda ilmi ya fi nagarta da inganci.
10. RASHIN DORA DALIBAI KAN HANYA: Akasarin daliban makarantun gwamnati duk ‘ya’yan talakawa ne. Da yawa iyayen su na tura su makarantar ne kawai don kada su zauna cikin unguwa su sangarce, amma ba don su zama wani abu a gaba ta dalilin cin moriyar ilimi ba.