Najeriya za ta hada kai da kungiyar ‘WAVE’ don hana shigowar Cutar Rogo

0

Hukumar kula da hana yaduwar cututtukan dake kama kayan abincin da ake hakowa na Najeriya ‘WAVE’ ta sanar da bullowar wasu cututtuka biyu dake kama rogo.

Shugaban hukumar WAVE Justin Pita ya sanar da hakan a taron masu ruwa da tsaki na kudu da Saharan Afrika da aka yi a Abuja ranar Litini.

Justin Pita yace cututtukan masu suna begomovirus nayi wa rogo illar gaske sanna ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta yi kokarin samar da hanyoyi domin hana cutar shigowa kasar nan.

Daga karshe ministan Ayyukan gona Audu Ogbeh ya mika godiyarsa ga hukumar ‘WAVE’ da irin kokarin da take yi a kasar nan kuma ya ce gwamnati za ta ba kungiyar hadin kai 100 bisa 100 don ganin cutar bata shigo kasar ba.

Share.

game da Author