Hukumar NAFDAC tare da ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Neja sun kona lalatattun magunguna da suka kai Naira miliyan 11.5.
Bisa ga rahoton gidan jaridar ‘Punch Newspaper’ shugaban ma’aikatar Mohammed Makunsidi ya ce sun kama magungunan ne a dakunan ajiyan magungunan da wasu asibitoci a jihar.
Ya ce cikin magugunan da suka kona akwai na cutar kanjamau, tarin fuka,ababen tsaftace hannu da sauransu.
Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta samar da kudade don yin irin wanna aiki saboda kare lafiyar jama’an jihar.