A daren Lahadi ne wani jirgin ruwa a rafin Neja dake karamar hukumar Yauri jihar Kebbi ta kife inda mutane 7 suka bace.
Wakilin Sarkin Ruwan Yauri da shugaban ‘yan jirgin ruwan Yauri Abdullahi Takwa ya tabbatar da hakan wa gidan jaridar PREMIUM TIMES ranar Litini.
Ya bayana cewa jirigin ruwan ta kife ne da wasu mutane ‘yan gida daya a lokacin da suke dawowa da ga shuka albasa a gonarsu dake Rokunalo.
‘‘Sanadiyyar wata iskar ruwa ne mai karfi ta sa jirgin kife’’.
Da gidan jaridar ta yi hira da shugaban karamar hukumar Yauri Musa Mohammed ya ce jirgin na dauke da mutane 9 wanda 7 daga cikin su sun bace amman an tsamo biyu daga cikinsu da ransu.
Discussion about this post