Akalla mutane shida ne suka rasa rayukan su a rikici tsakanin manoma da makiyaya a jihar Adamawa.
Rikici na farko ya auku ne a kauyen Sangere inda wasu manoma suka zargi wasu Makiyaya da laifin shiga musu gonaki da barnata musu amfanin su.
Wani mai gadin gonan mai suna Nathan Gibson da ya nemi ya hana su shiga gonan nan take ko ya gamu da ajalin sa.
Wasu ‘yan uwan Nathan hudu da suke aiki a gonakin su a kauyen Tudun Hassan suma basu sha da ran su a harin da Fulani suka kai musu suna aiki a gonaki.
Sun nemi sanin me ya kawo makiyayan gonar daga nan ne fa suka hau su da duka da sara jar sai a suka ga bayan su.
Suma jami’an tsaro na Civil Defence basu sha da dadi ba a wannan hari domin bayan sun yi kokarin Kai wa manoman dauki, makiyayan sun yi musu kwantar bauna inda suka yi ta yi musu ruwan kibau. Wasu biyu daga cikin su sun sami raunuka suna kwance a asibiti a Yola.
Discussion about this post